Wani Tsohon dan majalisar wakilai mai suna Tayo Sarumi ya rasu.
DAILY POST ruwaito cewa, ta samu labarin cewa Sarumi ya rasu da yammacin jiya Juma’a.
KARANTA WANNAN LABARIN: Zaben 2023: Wani A Fadar Shugaban Kasa Na Goyon Bayan Atiku – Wike
Dimokuradiyya ta gano cewa, Sarumi ya wakilci mazabar Ibadan ta Arewa tsakanin shekarar 2003 zuwa 2007.
Ya gaji dan uwansa, Hunorabul Alli Balogun, wanda ya wakilci mazabar tsakanin shekarar 1999 zuwa 2003.
Sarumi ya rasu yana da shekaru 75 a duniya.
Waheed Aderemi Gbede ne ya gaje shi wanda ya wakilci mazabar tsakanin shwkarar 2007 zuwa 2011.
Majiyoyi na kusa da dangin sun ce za a yi jana’izar tsohon dan majalisar a yau Asabar.
A WANI LABARIN KUMA: Fasinjoji 20 Sun Kone Kurmus A Wani Hatsarin Mota
Akalla fasinjoji 20 ne aka ruwaito sun kone kurmus da wuta da ransu a ranar Juma’a sakamakon wani mummunan hatsari da ya afku a yankin Ibarapa na jihar Oyo.
DAILY POST ta ruwaitocewa hatsarin ya afku ne da yammacin ranar Juma’a.