Shahararriyar yar Jaridar nan dake aiki da tashar watsa labarai ta Jihar Adamawa dake Yola, Amra Ahmad Diska ta samu kubuta daga hannun masu garkuwa da ita a sanyin safiyar yau laraba.
Ita Amra wacce aka garkuwa da ita a ranar hudu ga watan Mayun da muke ciki, tan aiki ne a matsayin Edita a tashar watsa labarai ta Jihar Adamawa wato Adamawa Broadcasting Corporation ABC, kana mai jego ce da bata wuce wata shida ba.
Labarin sakin nata ya buwayi gari ne da tsakar daren jiya wayewar garin yau, daga mai gidanta mai suna Alhaji Ahmad Mbamba.
“Alhamdulillah muna godiya, Amra ta kubuta kuma yanzu haka tana cikin iyalanta, Mun gode matuka da irin addu’o’in da jama’a suka yi ta yi mana” Cewarsa.
Har yanzu dai da muke kawo muku wannan rahoto, ba mu samu bayanan ko an biya kudin fansa gabannin sakin nata ba, to sai dai wasu majiyoyi sun tabbatar da cewa mutanen da suka yi garkuwa da itan sun bukaci a basu Naira dubu hamsin, kafin daga bisani suka rage shi izuwa dubu ashirin da biyar.
Sai dai daga mai gidan nata ya karyata wannan rahoto, inda ya ce na kanzon kurege ne kurum.