By Abbas Yakubu Yaura
A ranar Talata ne wasu fursunoni hudu suka mutu a gidan yari na Kosere, Ile Ife, dake jihar Osun, a wani yunkurin fasa gidan yarin da suka yi.
Wata majiya mai karfi ta jami’an tsaro ta shaida wa wakilinmu cewa wasu fursunoni sun shirya tserewa a lokacin da ake gudanar da tsaftar muhalli da safe.
Majiyar ta ci gaba da cewa fursunonin sun yi yunkurin tserewa daga cibiyar sun raunata wani jami’in tsaro kuma suna shirin ficewa ne yayin da jami’an tsaro suka dakile su.
Majiyar ta ce, “An kashe fursunoni hudu, An kuma jikkata wani mai gadi a cikin lamarin daya faru a lokacin tsaftar gidan yarin da safe a ranar Talata.
“Sun yi shirin tserewa ne, sai daya daga cikin su ya kai hari ga maigadi, yayin da wasu suka tilasta musu a hanyar kofar shiga daya tilo, amma jami’an tsaro sun dakile su, kuma ana cikin haka, an harbe fursunoni hudu.
“A ƙarshe sun mutu.wasu da suka so tserewa a lokacin da aka harbe wadanda suka jagoranci yunkurin.”
Jaridar Dimokuradiyya ta kuma samu labarin cewa Kwanturolan gidan gyaran hali na jihar Osun, Lanre Amoran, ya ziyarci cibiyar domin tantancewa a kai a kai.
Amma da aka tuntubi kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Osun, Sola Adeotan, ya ce basu da labarin faruwar lamarin.
Sai dai jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, Yemisi Opalola, ya tabbatar da faruwar lamarin, amma ya roki karin lokaci domin samun cikakken bayani.
“Ya faru amma ba a samu cikakkun bayanai ba tukuna, Zan dawo da zarar na samu karin bayani,” in ji Opalola.