Kungiyar dillalan man fetur ta Enugu karkashin kungiyar dillalan man fetur ta kasa IPMAN, ta shawarci masu ababen hawa da masu gudanar da zabe a jihar Anambra da su sayi isasshen man fetur a yau.
Shugaban IPMAN na shiyyar, Mista Chinedu Anyaso ne ya sanar da hakan a jiya a wata hira da kamfanin dillancin labarai na Ƙasa (NAN) a Awka, babban birnin jihar.
Anyaso ya ce matakin rufe cibiyoyin ya yi dai-dai da umarnin gwamnatin jihar Anambra na cewa yau da gobe a zamanto babu aikin yi domin baiwa ma’aikata damar zuwa wuraren da za su kada kuri’a.
Ya ce ‘yan sanda sun kuma ba da umarnin rufe baki daya wajen sana’o’i a jihar daga yau kuma mambobin su dole suyi biyayya ga dokar da aka sanya.
DUBA WANNAN LABARIN: Siyasa ba za ta hana Ni harkar fim ba – inji Sani Musa Danja
Shugaban ya bukaci ‘yan kasuwar da su bar ma’aikatansu da masu aikin gidan Mai, wadanda suka cancanci kada kuri’a, da suma su gudanar da ayyukansu na jama’a.
Anyaso ya tabbatarwa da jama’a cewa akwai wadataccen kayayyaki a jihar Anambra kuma masu bukatar kayan masarufi su je kowane shago su saya don gudun gararanba a goben.