Tsohon Ministan Sufurin Jiragen Sama a Najeriya Femi Fani-Kayode na ci gaba da shan suka biyo bayan yi wa wakilin Daily Trust da cin mutunci a bainar jama’a.
Ɓullar bidiyon a ranar Talata na cin zarafin da Femi Fani-Kayode ya yi wa wakilin Daily Trust a birnin Kalabar na Jihar Kuros Riba Charles Eyo ya jawo masa zagi daga hukumomin da ƙungiyoyi daga faɗin duniya da kuma sauran jama’a musamman a shafukan sada zumunta.
A taron ‘yan jarida da yake yi a Kalaba, a ci gaba da ziyarar jihohi da yake yi domin duba ayyukan gwamnoninsu, Charles Eyo ya tambayi tsohon ministan manufar ziyarar da kuma wanda ke ɗaukar nauyin tafiye-tafiyen nasa.
Amma maimakon bayar da amsa sai kawai Fani-Kayode ya ce wa ɗan jaridar ‘sakarai, dakiki’.
“Wane irin daƙiƙanci ne wannan? “Kar ka kuskura ka sake yi min haka. Bani da haƙuri, jikinka zai gaya maka”.
Ya ci gaba da yi wa Charles ruwan ashariya da munana kalamai da kuma barazana, amma ɗan jaridar bai tanka masa ba.
Sai da sakatare yaɗa labaran gwamna Ben Ayade, Christian Ita da sauran ‘yan jarida suka sa baki kafin fusataccen tsohon ministan ya ƙyale ɗan jaridar na Daily Trust.
Ita kuwa ƙungiyar rajin yaƙi da cin hanci da rashawa ta SERAP ta yi tir tare sa alawadai da cin mutuninci da Fani-Kayode ya yi wa ɗan jaridar sannan ta buƙace shi da ya nemi yafiyar ɗan jaridar.
“Kada wani ya sake ya kira wani ɗan jarida ‘sakarai’, saboda kawai ɗan jaridar na yin aikinsa”, inji SERAP.
Mutane da dama na ci gaba da bayyana ra’ayoyinsu dangane da faruwar lamarin.
Sai dai Femi Fani Kayode ya fito ya bayyana nadamarsa a shafinsa na twitter bisa wannan katoɓara da ya tafka, kuma ya nemi afuwar ɗan jaridar tare da dukkanin wanda ya ɓatawa rai a sakamakon lamarin.