• Zuba Bola barkatai ya addabi rayuwar al’umar Kuje dake babban birnin tarayya Abuja.
• “Ya kamata mahukunta su kaiwa yankin dauki daga wannan barazanar dake damun su.” Inji wani mazaunin yankin.
• “Zuba bola a bainar jama’a na da matukar olla ga rayuwar Dan’Adam” inji shi.
Samun karuwar yawan Al’ uma a yankin Kuje da ke babban birnin tarayya Abuja, ya haifar da samun zuba bola a bainar jama’a, da kuma Titin dake Kai matafiya zuwa Filin tashi da saukar jiragen sama dake Abuja.
Mazauna garin sun ce, zuba bola na kara zama ruwan dare a yankin, inda bolar ta ke zuwa wasu manyan hanyoyin da ke yankin.
Wani mazaunin yankin da ke Kwatas din Filin kwallon kafa na Kuje Township Mr Silas Jigo ya ce, Lamarin na kara kazanta a yankin, inda kuma ya yi kira ga mahukunta babban birnin tarayya Abuja dasu kawo dauki, domin magance matsalar da yankin ke fuskanta.
Ya ce ” Duba da irin illolin da ke tartare da lamarin ga lafiyar dan’Adam, Mahukunta yankin ya kamata suyi duk Mai yiwuwa wajan fitar da yankin daga irin barazanar dake fuskanta, na zuba bola barkatai” inji shi.
KARANTA : Yana da matukar wahala kasamu riba yanzu a harkar fim- cewar wata Jaruma.
Wata mazauniyar yankin na Kuje da ke Unguwar Kayarda Mrs Racheal Azihgbe, ta koka kan yadda ake zubar da bola barkatai a yankin, inda ta bayyana lamarin a mastayin abun kazanta.”