Akwai yiwuwar ɗan wasan tsakiya na kulob ɗin Manchester United, Christian Eriksen, ba zai sake buga wasa a wannan kakar ba ssboda raunin da ya samu.
Ɗan wasan na ƙasar Denmark mai shekara 30 a duniya ya samu raunin ne a yayin wasan da Manchester United tayi da Reading a gasar kofin FA na Ingila.
KU KARANTA KUMA: Ta mori miji: Wata budurwa ta fashe da kuka bayan ganin sha tara ta arziƙi da mijinta yayi mata
Man United ta bayyana cewa zai jinyar sa zata tsawaita wacce ka iya kai wa har zuwa ƙarshen wata Afrilu ko farkon watan Mayu. Rahoton jaridar The Tribune ya tabbatar.
“Sai dai, ana fatan cewa Christian zai dawo kan lokaci domin buga wasu wasannin ƙarshe na wannan kakar.” A cewar sanarwar da kulob ɗin ya fitar.
Ɗan wasan na tsakiya ya zama wani wanda ake damawa da shi a ƙarƙashin Erik Ten Hag, inda ya taka leda sau 31 a wannan kakar.
Kocin Al-Nassr Ya Bayyana a Inda Cristiano Ronaldo Zai Kawo Ƙarshen Buga Kwallon Sa
A wani labarin na daban kuma mai horar da Al-Nassr ya magantu a kan inda Cristiano Ronaldo zai aje wasa.
Mai horar da ƙungiyar Al-Nassr ta ƙasar Saudiyya, Rudi Garcai, ya bayyana a inda Cristiano Ronaldo zai kammala taka leda.
Rudi Garcia ya bayyana cewa Cristiano Ronaldo zai koma nahiyar Turai kafin ya daina buga kwallo, inda yayi nuni da cewa ɗan wasan ba zai kawo ƙarshen buga kwallor sa a ƙasar Saudiyya ba.