Wani ma’aikacin yanar gizo, Chizitere Ahubelem ya janyo cece-kuce yayin da ya bayyana yadda wata mata ta ba shi sharudda kafin ta yarda ta taimaka masa, Legit.ng ta ruwaito.
Kamar yadda ya bayyana, tare da wallafa hirar da suka yi ta WhatsApp, sai da ta nemi kwanciya da shi kafin ta tallafa masa da kudi.
KU KARANTA: Kin yi dace: Budurwa ta wallafa yadda kuɗin saurayinta ya wanketa, ta yi kyau da sheƙi
Ya sanar da Legit.ng cewa ya shiga matsanancin rashin kudi ne hakan ya na ya nemi tallafi daga wurinta.
A nan ne yace yana fatan kada Ubangiji ya sanya shi a yanayin da mai taimakonsu zai nemi lalata da shi kafin ya duba masa.
Matashin wanda ya yi fice a dandalin Facebook, ya wallafa yadda matar wacce bai sanar da sunanta ba ta nemi yin lalatar da shi saboda ya kaskantar da kan shi wurinta yana neman taimako.
Ya ce ta amsa cewa tabbas za ta taimaka masa amma ita ma sai ya taimaka mata ya yi lalata da ita na tsawon kwanaki.
Don tabbatar da gaskiyar yadda kamarin ya auku, Legit.ng ta nemi jin ta bakinsa ranar Alhamis da rana, inda ya ce gaskiya ne.
Ya ce a lokacin ba ya da kudin da zai iya amfani da shi a manhajar wayarsa, kuma yana jin gandar zuwa POS. Hakan yasa ya nemi tallafinta.
Yadda Saurayi Ya Yiwa Wacce Zai Aura Bazata Ya Cafke Ta Tana Sheƙe Aya a Otal
Wani ɗan Najeriya wanda yake zaune a ƙasar Turkiyya, ya kama wacce zai aura tana sheƙe ayar ta a otal.
Asirin budurwar ya tonu ne a cikin wani gwajin riƙon amana da wata mai ɗaukar bidiyo mai suna Sonia ta haɗa. Jaridar Legit.ng ta rahoto.
A cewar Sonia, matashin yana turowa budurwar ta sa kuɗin kula da kanta kowane wata, sannan ya buɗe msta shagon sayar da kaya na N6.5m a Najeriya, amma ta yarda ta ƙarbi dubu ɗari da hamsin domin a sheƙe aya da ita a otal.