Ɗan takarar gwamnan jihar Kogi a ƙarƙashin inuwar jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Usman Adodo ya cire hular sa sannan ya ɗuka a gaban zaɓaɓɓen shugaban ƙasa, Bola Tinubu.
Usman Ododo ya ɗuka a gaban zaɓaɓɓen shugaban ƙasar nw, ranar Asabar yayin da ya kai masa ziyara, rahoton jaridar Daily Trust ya tabbatar.
KU KARANTA KUMA: Gobara ta yi mummunar barna a fadar wani babban basarake
Ododo, wanda ya lashe zaɓen fidda gwanin gwamnan jihar na jam’iyyar APC, ya samu iso ne zuwa ga zaɓaɓɓen shugaban ƙasar lokacin da gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya gabatar da shi.
Kakakin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila da shugaban jam’iyyar APC na jihar Kogi, Abdullahi Bello, suna daga cikin waɗanda suka tattauna da Ododo a lokacin ziyarar.
Tinubu, yayin da ya ke taya Ododo murna ya ɗaga masa hannu sama domin nuna amincewa da yarda da takarar sa.
Domin nuna godiyar sa, Ododo ya coew hular sa sannan ya ɗuka a gaban zaɓaɓɓen shugaban ƙasar.
Abba Gida Gida Zai Binciki Batun Tsige Sarki Sunusi – Kwankwaso
Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP kuma jagoran tafiyar Kwankwasiyya, Rabi’u Musa Kwankwaso, ya ce gwamnati mai zuwa a Kano za ta sake duba batun tsige Sarkin Kano Muhammadu Sanusi na 14.
Sanusi wanda ya zama sarki a wa’adin karshe na Kwankwaso a matsayin gwamna, Gwamna mai barin gado Abdullahi Ganduje ne ya tsige shi, wanda shi ne mataimakin gwamna a lokacin da aka nada sarkin.