Wani bidiyo ya yi matukar daukar hankalin mutanen shoshiyal midiya bayan ganin wata amarya cike da farinciki mara misaltu.
A bidiyon wanda take sanye da kaya launin farare da alamu ranar aurenta ne ya dauki hankali, shafin Gaskiya zalla na Instagram ya wallafa.
KU KARANTA: Garin neman gira: Ango ya sha ƙasa yayin ƙoƙarin ɗaga amaryarsa
A bidiyon an ga yadda ta kasa boye farincikinta inda ta kwashi rawa tana daga hannunta sama tana godiya ga Ubangijin da ya nuna mata ranar aurenta.
Ko da gani tana matukar kaunar angon nata mai suna Abba wanda hakan yasa ta kasa boye murnar. An ji tana cewa:
“An daura an daura, na zama matar Abba. Allah Nagode maka.”
Wannan bidiyon ya dauki hankali sosai. Wasu na ganin rashin kunya ne tayi. Inda wasu kuma ke ganin tsabar siyayyar da ke tsakaninta da angonta ne ya janyo hakan.
Bidiyo: Yadda Baƙuwa Ta Rika Taba Wa Amarya Wuraren Albarkatunta a Wurin Biki Ya Ja Hankali
Wani faifan Bidiyon ya nuna yadda wata mata ta taba wata amarya a wuraren albarkatunta a wajen daurin aure a cocin dake Enugu-Ukwu, jihar Anambra, ya jawo hankalin amaryar.
A cikin wani faifan bidiyo da wani magidanci ya dauka, an ga wata bakuwa mace ta nufo amarya, Maimakon ta rungumi amaryar kamar yadda sauran baƙi suka yi, sai kawai matar ta miƙe ƙasa ta taɓa wurin da bai dace a jikin amarya.