Wata budurwa ta rikice bayan karenta ya lalata mata wayarta kirar IPhone 14 Pro Max kuma ta yanke masa hukunci mai tsanani, intel region ta ruwaito.
KU KARANTA: Yadda budurwa ke kwalliya kamar budurwa ya ɗauki hankali
Budurwa ta wallafa bidiyonta a yanar gizo tana nuna yadda ta daura wa karen sanda a wuya tare da daure masa kafa da kyalle da bindi inda ta nemi ya yi tafiya a haka.
Ya bayyana yadda ya lalata mata wayarta mai tsada bayan tattara kudade daga wurin mutane daban-daban wurin siya.
Ta ce ta yanke shawarar azabtar da shi a haka yadda nan gaba idan ta siya wata wayar ba zai yi gigin tabawa ba.
Nan da nan mutanen soshiyal midiya suka hau tausaya wa karen inda suka ce ba zai lalata wayar bisa ganganci ba.
Wasu kuma sun kwashi nishadi ne inda suka dinga tsokaci mai ban dariya.
Masu son bidiyon tsiraicina su tura min saƙon kai tsaye, Budurwa ga mabiyanta na TikTok
A bidiyon nata wanda wani shafin Aisha Fulani ta saki, an ji yadda ta ke cewa ga masu bukatar bidiyon tsiraicinta su yi mata magana.
Bidiyon ya yi matukar ba da mamaki kasancewa yawancin masu tura bidiyon tsiraicinsu ba sa bayyana wa duniya sai dai a ha’ince su a saki.