• An yi dauki badadi bayan Yan bindiga sun sake farmakan wani yanki a Abuja da Jami l’an soji.
• Lamarin ya farune a yankin Tungan-Maje dake Babban birnin tarayya Abuja, inda yan’bindigan su ka dawo yankin awanni 48 bayan sun yi garkuwa da Mutane 6.
• Sai dai haryanzu Mai magana da yawun rundunar yan sandan Abuja ba ta ce komai ba dangane da harin.
Wasu yan bindiga da ake zargin masu Garkuwa da mutane ne sun sake afkawa garin Tungan-Maje dake Babban birnin tarayya Abuja a daren jiya Laraba, kasa da awanni 48 ke nan bayan sun yi garkuwa da mutune 6 a yankin.
Wani mazaunin yankin Mai suna Abdullahi Aliyu ya ce, masu Garkuwa da mutanan sun shiga Anguwar Dabiri da Anguwar Samu, Wanda ke kusa da birnin da musalin karfe 10:48pm na dare, inda suka fara harbin iska, domin tsoratar wa.
Ya kara da cewa, wasu jami’an soji da aka jibge a wajan garin, nan take su ka Maida wa yan bindigan wuta, inda hakan yasa batare da shi ba su ka tsere, domin tsira da rayuwar su.
” Maganar gaskiya ita ce, Masu Garkuwa da mutanan sun dawo ne, domin sun farmaki wasu gidage dake Anguwar Dabiri da Anguwar Samu, Wanda ya gagare su sakamakon taimakon jami’an soji.” Inji shi.
KARANTA WANNAN LABARIN: Dalibai biyu na makarantar Bathel Baptist sun shaki iskar yanci
Kazalika ya ce, al’umar yankin, musamman ma wadanda su ke kusa da inda lamarin ya faru, sun shiga cikin firgici, sakamakon tsananin karar harbe-haben da ya wakana tsakanin yan bindigan da jami’an sojin.
“Za ka iya tunanin cewa, ko Tungan-Maje ya zama wani fagen daga ne, sabida musayar wutar da kuma dauki ba dadin da ya wakana tsakanin Masu Garkuwa da mutanan, da kuma soji” inji shi.
Mai Magana da yawun rundunar yan sandan babban birnin tarayya Abuja ASP Maryam Yusuf, wacce ta bukaci wakilin jaridar Daily Trust, da ya tura mata sakon kartakkwana, haryanzu bata ce komai ba kan faruwan lamarin.
Comments 2