Baka da hannu wajan yakin neman zaben mu, Yan majalisu ga Lai Muhammad
Yan majalisun Jahar Kwara, a jiya suka ce “Ministan labarai da al’adu Lai Muhammad bai dauki nauyin yakin neman zaben mu ba kamar yadda yake bayani.”
Sun ce wannan kanzon kurge ne, kan yadda yake bayyanawa ya dauki nauyin yakin neman zaben Yan majalisun.
KARANTA:-Na’urorin mu ba na sayarwa bane, KEDCO
Yan majalisun sun ce ” Wanda zai tutiyar ya bada babban taimako wajan yakin neman zaben mu bai wuce gwamna AbdulRahman AbdulRazaq ba wanda dankara ne a jam’iyyar APC a lokacin.”
Hon. Yakubu Danladi Salihu, ke bayyana haka ga manema labarai a birnin Illorin babban birnin Kwara, inda yake cewa Ministan bai taimaki Yan majalisun ba ta kowanne hanya.”
Yayi kira ga jama’a da su dauki wannan a matsayi tatsuniya ba sahihin labari bane.
Comments 1