Ƴan Najeriya sun tsinci kan su cikin wani matsanancin hali a dalilin sauya takardun kuɗin naira da babban bankin Najeriya (CBN) yayi.
Babban bankin na Najeriya ya sauya takardun kuɗi na naira inda aka fito da wasu sababbi waɗanda za su maye gurbin su.
Sai dai fitowar sababbin kuɗin ta zo da tarnaƙi inda samun su a bankuna ya zama wani babban aiki ja.
KU KARANTA KUMA: Ciwo ba nakasa bane: Bidiyon wata budurwa mara hannuwa na kula da mijinta ya ɗauki hankula
Mutane na shan baƙar wahala kafin su samu kuɗi a bankuna yanzu wanda hakan har ya kai ga ya fusata wasu, inda har suka ba hammata iska a cikin banki.
Wani bidiyo dake yawo a kafafen sada zumunta ya nuna lokacin da mutane biyun suka kaure da faɗa a cikin harabar wani banki.
Faɗan na su dai ya kaure ne a gaban mutane da kuma ma’aikatan bankin waɗanda suka tsaya suna kallon ikon Allah.
Ku kalli bidiyon a nan:
Sababbin Kuɗi: Mata Mai Juna Biyu Ta Mutu Bayan Mijinta Ya Kasa Ciro Kuɗi a Banki
A wani labarin na daban kuma, wata matar aure mai ɗauke da juna biyu ta rigamu gidan gaskiya saboda mijinta ya kasa ciro kuɗi a banki.
Wata matar aure mai ɗauke da juna biyu ta mutu bayan mijinta ya kasa samo kuɗi a banki waɗanda zai biya domin a duba lafiyarta.
A cewar rahoton majiyar mu lamarin ya auku ne a Kasuwan Magani, cikin ƙaramar hukumar Kajuru ta jihar Kaduna.
Mijin matar, James Auta, ya bayyana yadda asibiti suka ƙi karɓar matar tasa saboda bai biya kuɗin da zaa duba ta saboda ƙarancin takardun kuɗin naira.