Wani dan Acaban mai suna Arabo Dauda, ya gamu da ajalinsa ne a madakatar ‘yan sanda ta Maiha dake karamar hukumar ta Maiha a jihar Adamawa.
Dan Acaban mai Shekaru 20 da haihuwa ya rasa ransa saboda kin bada cin-hancin Naira 100.
Shugaban karamar hukumar ta Maiha Idi Amin ya tabbatarwa da manema labarai afkuwar lamarin a yau Talata.
Yace “ina zaune sai aka kirani wai ga wani dan sanda ya harbe wani matashi akan Naira 100”.
https://dimokuradiyya.com.ng/an-sake-kama-wani-dan-sanda-da-yayi-sanadiyyar-mutuwar-abokin-aikinsa/
“Dana yi bincike sai na gano cewa yaron yaki bada hadin kai ne wajen bayar da cin-hanci. Dan sandan ya harbi yaron ne a baya a yayin da ya dawo daga siyan man fetur akan hanyarsa ta komawa gida”.
“Ban bata lokaci na kira shugaban hukumar ‘yan sanda na shaida masa abinda ke faruwa”.
Sai dai kisan matashin ya bar baya da kura inda matasa suka fusata wajen daukar mataki har ta kai ga sun suka kona ofishin ‘yan sanda.
Jami’in da yayi kisa a yanzu yana hannun hukumar a babbar hedikwatar’yan sanda dake Yola babban birnin jihar ta Adamawa.