A ranar Lahadi ne jagoran jam’iyyar APC, Bola Tinubu, ya gana da shugaban kasa Muhammadu Buhari a Aso Rock
Tinubu ya gana da Buhari a fadar shugaban kasa a ranar Lahadi.
Tinubu da yake zantawa da manema labarai bayan kammala taron ya ce makasudin ziyarar tasa ba ta siyasa ce ba, illa maraba da Buhari daga tafiyar da ya yi zuwa kasar Saudiyya inda ya je aikin hajji.
Tsohon gwamnan na Legas ya ce ya kuma gode wa shugaban kasar da ya ziyarce shi a Landan bayan kammala aikin jinya.
Tinubu ya ce: “Ziyarar ta kasance ne kawai don gode wa shugaban kasa, da farko, saboda ziyarar da ya kawo min a gidana da ke Landan bayan tiyatar da aka yi min, da kuma yi min fatan alheri, ya kara min kwarin guiwa da kuma irin abin da shugaba na kwarai zai yi don hada kai.”
KARANTA WANNAN LABARIN: Masu Garkuwa sun yi Garkuwa da Limami da Ya’yansa 2 a Abuja
“Don haka abin da na zo yi kenan, da kuma yi masa maraba da dawowar sa daga Saudiyya.”
“Babu siyasa a ciki, kawai ziyarar girmamawa ne don gode masa, shi ke nan.” A cewar sa.
Idan za’a iya tunawa cewa, Buhari ya ziyarci Tinubu a Landan bayan tiyatar da aka yi masa a gwiwa.
Comments 1