Hukumar kula da zirga-zirgar jiragen kasa ta Najeriya NRC ta yi watsi da rahotannin dake cewa ta dakatar da zirga-zirgar jiragen kasa a kan titin Itakpe-Warri sakamakon harin da wasu ‘yan bindiga suka kai tashar jirgin Ekehen da ke karamar hukumar Igbuebem ta jihar Edo. Kamar yadda Channels TV ta ruwaito.
Manajan Darakta na Hukumar Kula da Jiragen Kasa ta Najeriya (NRC), Fidet Okhiria, ne ya shaida wa gidan Talabijin na Channels ta wayar tarho cewa ba a dakatar da ayyukan jiragen kasa ba, sabanin rahotannin da ake ya dawa.
KARANTA WANNAN LABARIN: Ziyarar Buhari: Gwamnatin Yobe Ta Ayyana Ranakun Hutun A Jihar
Ya tabbatar da cewa an kai harin wanda a halin yanzu ‘yan sanda da hukumar kula da zirga-zirgar jiragen kasa ta Najeriya NRC ke ci gaba da bincike, amma ya ce lamarin bai kawo cikas ga ayyukan tashar jirgin kasan ba.
Okhiria , ya kara da cewa kamfanin layin dogo na samar da matakan tabbatar da lafiyar fasinjoji.
A gefe guda kuma Rundunar ‘yan sandan jihar Edo a ranar Lahadin da ta gabata ta tabbatar da cewa wasu da ake zargin makiyaya ne sun kai farmaki tashar inda suka yi awon gaba da fasinjoji da dama da ke jiran hawa jirgin kasa zuwa Warri na jihar Delta.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Chidi Nwabuzor, yayin da yake tabbatar da faruwar lamarin, ya ce harin da aka kai da yammacin ranar Asabar, ya yi sanadin jikkatar mutane da dama.
A cewar rundunar ‘yan sandan, wadanda suka yi garkuwa da su dauke da bindigogi kirar AK-47, sun kutsa kai cikin tashar jirgin inda suka yi tabharbin tsoratarwa ba kakkautawa, kafin su yi awon gaba da matafiya da dama a cikin daji.
A wani labari kuma, Atiku Ya Yi Allah-Wadai Da Harin Jirgin Kasan Edo
Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, ya yi Allah-wadai da harin jirgin kasa na Edo, yana mai cewa “tunawa ne a kan bukatar gaggawar sake fasalin tsarin tsaron mu domin kare rayuka da dukiyoyin ‘yan Najeriya.”
Ku tuna cewa sama da fasinjoji 30 da ma’aikatan hukumar kula da layin dogo ta Najeriya (NRC) ne ake kyautata zaton an sace sakamakon farmakin da masu garkuwa suka kai a daren ranar Asabar a tashar jirgin kasa ta Igueben da ke jihar Edo.
Da yake mayar da martani, Atiku, a cikin wata sanarwa da ofishin yada labaran sa ya sanyawa hannu a ranar Lahadi, ya lura cewa wannan mummunan abu ne “shine na baya-bayan nan a cikin jerin tashe-tashen hankula na tsaro da ba a taba ganin irinsa ba a tarihin kasarmu.”