Babban lauyan nan Mai Muƙamin SAN, wato Femi Falana, ya baiwa kakakin yan Sanda na kasa wa’adin Sa’o’i 24 kan ya janye Kalamansa.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa Mai magana da yawun yan sandan a jiya wasu kalamansa, suka cika gari wanda yace farar hula laifi ne ya mari dan sanda dake cikin kayan sarki.
“Ko dan sanda sanye da kakin ya mari farar hula, farar hula ba shi da hurumin kara ramawa don haka idan yana sanye da kayan aiki, rashin mutuntawa ga Najeriya ne, duk dan sandan da ke sanye da kakin, amma kuma baya mutunta yan kasa.”
KARANTA ANAN: Majalisar Wakilai Za Ta Gana Da Masu Ruwa Da Tsaki Da Shugabannin ASUU
Femi Falana bai yarda da wannan kalaman ba, inda ya mayar da martani cewa: “Idan har ba a janye maganar nan da sa’o’i 24 masu zuwa ba, to babban sifeton ‘yan sandan Najeriya Usman Alkali Baba, bai kamata ya yi kasa a gwiwa ba wajen maye gurbin Mista Adejobi da wani dan sanda, wanda ya san mutuncin jama’ar kasa da martaba ƙimarsu.”
“Yayin da ake bukatar farar hula su mutunta jami’an ‘yan sanda, wadanda suke gudanar da ayyukansu bisa doka, sashe na 34 na kundin tsarin mulkin Nijeriya, ya bayyana cewa kowane dan kasa na da hakkin ya sami ‘yancin mutuntaka ta dan adam, yana mai cewa hukuncin cin zarafin farar hula ne,” Inji Falana.
A wani labarin kuma: A halin yanzu ana ci gaba da jana’izar Sarauniya Elizabeth ta biyu.
Ana gudanar da jana’izar Sarauniyar wacce ita ce sarki mafi dadewa a kan karagar mulki a birnin Landan.
Ta rasu ne a ranar 8 ga watan Satumba tana da shekaru 96, wanda ya bar mutane da yawa da yin jimamin rasuwarta duk da cewa mutane da yawa suna tunanin rayuwarta da irin rawar da ta taka a matsayin Sarauniya, ba kawai ta Burtaniya ba har ma a duniya.