Kwanaki kadan da suka wuce wasu dalibai suka rasa rayukansu a dalilin fyade a Ibadan, a wannan karon ma hukumar ‘yan sanda ta jihar Oyo ta sanar da mutuwar wata yarinya mai shekaru 21 a duniya wadda aka yi wa fyade a cikin majami’a.
Wace iftila’in ya afkawa mai suna Grace Oshiagwu, lamarin ya faru a unguwar Idi-ori dake kan titin Shasha.
Hukumar ‘yan sanda ta bayyana an samu raunkuka a kanta wanda yake nuni da cewa an sareta da wani abu mai kaifi, SP Gbenga Fadeyi, yace har yanzu ana ci gaba da bincike amma ba a gano wanda ya aikata lamarin ba.
“Yanzu haka ana gudanar da bincike amma dai ba a gano wanda yake da hannu a lamarin ba, zamu ci gaba da tattare bayanai daga mazauna yankin don ganin an damko wanda ya aikata wannan mummuna laifi”.