Gwamnatin jihar Taraba ta ba da umarnin buɗe makarantun firamare da sakandare a jihar ranar Litinin 21 ga watan Satumba, 2020.
Kwamishinan Ilimi a Matakin Farko na jihar, Johannes Jigem, ya bayar da umarnin buɗe makarantun a lokacin taron masu ruwa da tsakin a harkar ilimi a jihar.
“Muna umartar dukkannin makarantu da su jingine zangon karatu na uku da annobar Korona ta yi wa cikas.
“Buɗe makarantun a ranar 21 ga watan Satumba zai zama zangon karatu na farko ne kuma kuɗin zangon karatun da makarantu za su karɓa kenan.
“Gwamnati na ba wa iyaye kwarin gwiwar cewa su tura ’ya’yansu makaranta nan take”, inji kwamishinan.
Ya ce Gwamna Darius Ishaku na umartar dukkannin makarantun su bayar da muhimmanci ga kiyaye matakan kariyar Korona.
Jingem ya ce buɗewar ta keɓanci makarantun firamare da sakandare ne kaɗai, amma bai ce komai game da batun buɗe manyan makarantu a a Jihar ba.