Daga: Muhammad Gambo Damaturu
Kwamishinan Ma’aikatar kula da Kananan Hukumomi a Jihar Yobe Alhaji Yerima Lawan Mahmud, ya nisanta Ma’aikatar da Gwamnatin jihar Yobe da jinkirta albashin Ma’aikatan kananan hukumomin jihar.
Jaridar Dimokuraɗiyya ta rawaito cewa ya bayyana haka lokacin da yake amsa tambayoyin manema labarai, a wajen taron zayyana nasarori da ma’aikatun Gwamnati suka samu a shekarar da ta gabata karkarshin jagoranci Gwamna Mai Mala Buni.
“Babu shakka wasu lokuta ana samun jinkirin biyan albashin ma’aikatan kananan hukumomi, to amma hakan yana faruwa ne sakamakon matsalar hanyoyin biya na zamani(Technical issues) daga bankuna inda har ma a wasu lokutan kudaden sukan dawo (Reverse Alert)”, in ji Kwamishinan.
KARANTA ANAN: Barazanar Tsaro Ta Sanya DSS Buƙatar ASUU Ta Janye Yajin Aiki
Da yake zayyana irin nasarori da hukumar ta samu, Kwamishinan yace, a shekarar da ake ciki, Ma’aitar ta samo izinin samun kudaden yin ayyuka a fannuka daban-daban, kamar aikin samar da ruwa, kiwon lafiya, ilimi, noma, tsaro da sauran su.
Yace Gwamnatin yanzu, karkashin shugabancin Mai Mala Buni tana bada kyakkyawar kulawa ga Ma’aikatar kula da Kananan hukumomi da Masarautun gargajiya.
Ya ce a wannan shekarar da ake ciki, bayan biyan albashin Ma’aikatan Kananan Hukumomi, Ma’aikatar ta cigaba da aikin karin girma ga kananan asibitocin Yusufari da Machina zuwa matakin Manyan asibitoci.
Ta samar da kudaden gina masarautun Yusufari, Ngazargamu, da Masarautar Fune, tare da gina mazaunin ‘yan kallo a harabar wasanni dake garin machina.
Tun da fari a jawabin maraba, Shugaban kungiyar ‘Yan jarida ta Najeriya reshen jihar Yobe Comrade Rajab Muhammad ya godewa Kwamishinan kan amsa gayyatar da Kungiyar tayi masa.
A yayin taron, Kwamishinan yana tare da babban sakataren ma’aikatar da sauran manyan daraktoci.
A wani labarin kuma: ‘Yan Rasha 10,000 Sun Bukaci A Turasu Yaki A Ukraine
Bayan sanarwar da Rasha ta fitar a jiya na cewa za ta tura dubunnan dakaru domin yaki a Ukraine, kakakin rundunar sojin Rasha ya ce tuni ‘yan kasar Rasha 10,000 suka ba da kansu da kansu a ranar farko ta fara yada wannan gangamin. Kamar yadda BBC ta ruwaito.
“Kimanin ‘yan kasar 10,000 ne suka isa ofisoshin daukar Jami’an soji da kansu ba tare da jiran an kira su ba,” in ji Vladimir Tsimlyansky a cikin kalaman da kamfanin dillancin labaran Rasha Interfax ya nakalto.