Hukumar zaɓe ta ƙasa (INEC) ta buɗe shafi a yanar-gizo da za a rinƙa amfani da shi wajen duba sakamakon zaɓe domin inganta harkokin zaɓe a faɗin ƙasar nan.
Kwamishinan hukumar mai kula da yaɗa labarai da wayar da kan jama’a, Festus Okoye ya ce shafin zai fara aiki daga Asabar 8 ga watan Agusta a zaɓen cike gurbi na mazabar Nasarawa ta Tsakiya.
Ya ce harkar tafiyar da sakamakon zaɓe ya kasance daga cikin manyan ƙalubalen harkar zabe a Najeriya kuma “INEC ta ƙosa ta rika yin komai a fili a harkar zaɓen Najeriya, musamman wajen bayyana sakamako.
https://dimokuradiyya.com.ng/maaikatan-inec-sun-tsere-daga-wurin-zabe-bayan-sun-sha-bugu-a-kogi/
“Babban ginshiƙin dimokraɗiyya ne a ƙidaya ƙuri’u yadda ya kamata, wanda shi ya sa muka ƙirƙiro takardar EC 60E, wanda aka kwafo takardar EC 8A wanda za a riƙa liƙawa a wajen zaɓe”, cewar Festus.
Sai dai ya ce duk da hakan, akwai buƙatar ƙara inganta harkar tafiyar da sakamakon zaɓen, wanda shi ya sa INEC ta ƙirƙiro shi ta hanyar yanar-gizo wanda jama’a za su iya duba sakamakon mai suna IReV.
INEC ta ce IReV zai ba jama’a damar duba sakamakon zaɓen tun daga matakin mazaɓa da zarar an kammala kaɗa ƙuri’a.