Wani hoto ya bayyana yadda jami’an Hukumar Kulawa da Cunkuson Titina na Jihar Kano, KAROTA, suka yi ram da wani jaki, LIB ta ruwaito.
Kamar yadda lamarin ya auku, sun ga jakin ne a titi yana yawo yadda ya ga dama kuma akwai yiwuwar ya janyo hatsari a hanya.
KU KATANTA: Ɗan jaridar BBC ya ci na jaki yayin da ya je ɗaukar rahoton zanga-zanga
Wannan dalilin ne ya sanya suka yi gaggawar kama jakin inda suka saka shi cikin motarsu suka yi gaba.
Tuni hoton ya yadu ta ko ina a kafafen sada zumuntar zamani inda aka ga jami’an suna kama jakin.
Duk da dai baya ga yawo a titin babu wani laifi da ake zargin jakin ya yi musu, amma yanzu haka ana jiran yadda za ta kaya.
Har yanzu dai da wuya idan mai jakin ya kai kan sa wurin jami’an don jin dalilin da zai saka a kama masa dabba.
Matasa sun lakaɗa wa shugaban makarantar sakandare na-jaki bayan kama shi yana lalata da dalibarsa
Matasa sun kama wani mataimakin shugaban makarantar sakandare dumu-dumu yana lalata da dalibarsa, LIB ta ruwaito.
Mutumin wanda shi ne na biyu a matsayi a makarantar sakandare nan Kgagatlou da ke Polokwane, Limpopo ya ci na jaki bayan an kama shi yana lalata da dalibarsa yayin da wasu daliban ke karatu a azuzuwansu.