Jami’an ‘Yan sanda a jihar Anambra sun yi nasarar harbin wani barawo da yayi kwacen wata jaka dauke da kudi kimanin naira Miliyan 3.5 a daidai bankin new generation dake Awka.
Wani wanda ya ganewa idonsa faruwar lamarin, ya shaidawa Jaridar Punch cewa barawon mai suna Chukwuemeka Afor, ya dauki tsawon sa’o’i yana harbe-harbe tsakaninsa da jami’an’yan sanda.
“Ya fara harbi kan mai uwa da wabi, amma yan sanda sun samu nasara akansa saboda sun masa yawa kuma sun ji masa raunuka da yawa”.
https://dimokuradiyya.com.ng/yan-sanda-sun-hallaka-yan-fashi-uku-a-anambra/
Haruna Mohammed, wanda shi ne kakakin hukumar’yan sanda na jihar ya tabbatar da faruwar lamarin. Inda yace an kama barawon kuma kudin da ya sace an same su.
Mohammed yace akwai wanda suka samu rauni a sakamakon harbe-harben da aka yi, sai dai an dauke su zuwa asibitin ‘yan sanda dake Awka, shi kuma barawon ana ci gaba da bashi kulawa kafin kuma a tuhumesa bisa laifin da ya aikata.
Ya kara da cewa yanzu haka hukumar tasu na gudanar da bincike, kafin daga bisani a yanke hukunci akan lamarin.