•Gwamnan jihar Sokoto Aminu Tambuwal ya ce, an kama wanda ake zargi kuma ana cigaba da gudanar da bincike.
• Za’ a gurfanar da wanda ake zargi a gaban Kotu da zaran an kammala bincike domin ya girbi abun da ya shuka.
• Gwamnan jihar ya Kuma ya ba wa Matasan jihar bisa tuntubar hukumomin tsaro da sukayi maimakon su dauki doka a hannun su.
Gwamnatin jihar sokoto ta bukaci al’umar jihar, da su kwantar da hankalin su, domin kuwa gwamnatin jihar da hadin gwaiwar jami’an tsaron, da sauran masu ruwa da tsaki, su na bin hanyoyin da suka dace, domin tabbatar da gurfanar da wanda ake zargi da yin kalaman batanci ga fiyayyan halitta Annabi Muhammad S.A.W a gaban Kotu.
Gwamnatin jihar ta bayyana hakan ne, a cikin wata sanarwa da tasami sa hannun Kwamishinan yada labarai na jihar Isa Bajini Galandachi ya fitar, a madadin gwamnan jihar Aminu Tambuwal, inda Gwamnan ya yi Alllah-wadai da mummunan dabi’ar wanda ake zargin.
Kwamishinan ya ce, Gwamnan jihar Aminu Tambuwal ya yi jan hankali kan gujewa siyasantar da lamarin, inda ya bukaci hadin kan Al’uma dangane da irin wannan lamari.
Ya kara da cewa Gwamnan jihar, ba zai lamunci kalaman batanci ba, ga Fiyayyan halitta Annabi Muhammad S.A.W, ko wani Annabin Allah, ko kuma wasu littattafan sa.
KARANTA WANNAN LABARIN: Sarkin Musulmi ya bukaci a duba wata a yau
A cewar Kwamishinan, Tuni a ka kama wanda ake zargin, Kuma a na cigaba da gudanar da bincike, inda ya ce, da zaran an kammala za’a gurfanar da shi a gaban Kotu, domin ya girbi abun da ya shuka.
A karshe ya ce, Gwamnan jihar ya yaba wa hadakar Matasan jihar, bisa yunkurin da suka yi na kauracewa banbance- banbancen dake tsakanin su, da kuma hada kan su, wajan tuntubar hukumomin tsaro, sabanin daukar doka a hannun su.
Comments 1