Gwamnatin jihar Kaduna ta janye dokar hana sallah a masallatai da majami’u dake faɗin jihar ta Kaduna tare da jadadda bin ƙa’idojin kaucewa kamuwa da cutar ta Korona.
A wata sanarwa da ke ɗauke da sa hannun mai baiwa gwamna El-Rufa’i shawara yaɗa labarai Muyiwa Adekeye ya ce janye dokar ya biyo bayan shawarar da kwamitin yaƙi da cutar a jihar ya bayar ne.
Wasu daga cikin ƙa’idojin da gwamnatin ta ce dole a riƙa bi sun haɗa da: sanya takunkumi da ba da tazara da wanke hannu lokaci zuwa lokaci da kuma kaucewa cinkoso da sauransu.
https://dimokuradiyya.com.ng/watakila-mu-sake-saka-dokar-kulle-a-kaduna-gwamna-el-rufai/
El-Rufai ya kuma yi gargaɗin cewa za’a rufe duk masallacin da ya ƙi bin dokoki ko ƙa’idojin da aka gindaya.
Idan ba’a manta ba gwamnatin jihar ta hana Sallah a masallatai ne tun a watan Maris na shekarar nan da muke ciki a wani yunƙuri na daƙile yaɗuwar cutar Korona a jihar.