‘Yan Najeriya 317 ne gwamnatin tarayya ta bada umarnin kwasowa daga kasar Birtaniya bayan ɓulllar cutar Koron ta ritsa da su a can.
Sanarwar da gwamnatin tarayya ta fitar, ta ce kananan yara guda 9 na daga cikin waɗanda aka kwaso.
https://dimokuradiyya.com.ng/dokar-kulle-najeriya-ta-sake-kwaso-mutane-102-daga-kasar-masar/
A ranar Lahadi ne Ministan Harkokin Waje, Geoffrey Onyeama ya sanar a shafinsa shafinsa na Twitter, cewa 175 daga cikin fasinjojin sun sauka ne a Abuja, kafin jirgin ya karasa Legas ya sauke sauran 142 din.
Ministan wanda ya ce jirgin ya samu jinkiri saboda wasu dalilai, ya kara da cewa dukkannin waɗanda suka dawo ɗin za su killace kansu na kwanaki 14 kamar yadda hukumomin lafiya suka tsara domin tantance ingancin lafiyarsu, kafin su shiga cikin jama’a domin ci gaba da rayuwa.