Wata babbar kotu dake zamanta a jihar Ondo ta yankewa wani malamin addinin kirista mai suna Fasto Kolawole Samson hukuncin kisa ta hanyar rataya bayan da aka same shi da kisan Ayo Olaniyi a yankin Okeigbo dake jihar shekaru hudu da suka wuce.
A yayin da mai shari’a Ademola Bola yake sauraron karar, ya bayyana cewa kotun ta kama malamin da laifin saran mamacin da adda a kai wanda yayi rasuwarsa a asibiti.
Lauyan da yake daga bangaren gwamnati ya bayyana kotu cewa an sari mamacin da adda ne a lokacin da yaje farautar Kwadi.
https://dimokuradiyya.com.ng/yan-bindiga-sun-kashe-mutane-13-a-katsina/
Kotun ta bayyana cewa laifin ya sabawa sashi na 316 karkashin sashi na 319 na kudin laifuka na 37 na jihar.
Sai dai wanda ake zargi da laifin ya musunta zargin da ake akansa.
A yayin da ake sauraron shari’ar jiya, Alkalin kotun ya bayyana cewa dukkanin bayanan da aka gabatar a gaban kotun shekaru hudu da suka wuce zuwa yanzu sun nuna malamin shi ne wanda ya kashe mamacin.
Mai shari’a Bola ya yankewa Samson Kolawole hukuncin kisa ta hanyar rataya.