Daraktan wasanni na Paris Saint-Germain, Luis Campos ya ce ba a yanke shawara kan makomar kocin kungiyar, Christophe Galtier ba,Daily Post ta rawaito.
Zakarun na Ligue 1 sun kammala kakar wasansu da ci 3-2 a hannun Clermont Foot.
KARANTA WANNAN: Dalilin Da Yasa Arsenal Ta Barar Da Damar Lashe Gasar Premier — Arteta Yayi Bayani Dalla-Dalla
Galtier ya samu nasarar lashe kofin gasar bana ne kawai ga PSG, inda ya kasa tsallakewa zuwa zagaye na 16.
An dai yi ta rade-radin cewa kungiyar za ta kori Galtier, inda aka yi hasashen kocin Roma Jose Mourinho zai maye gurbinsa kafin kakar wasa mai zuwa.
Amma Campos ya gaya wa Canal Plus ranar Asabar cewa, “Ba mu yanke shawara ba, ko kan kocin ko ‘yan wasan.”
Hakan ya faru ne a ranar da Lionel Messi da Sergio Ramos suka buga wasanninsu na karshe a kungiyar.
Dukansu Messi da Ramos sun bar Parc des Princes a matsayin wakilan kyauta.
A wani labarin kuma, EPL: Arteta Ya Bayyana Kungiyoyi Biyu Da Suka Ci Nasara Kan Arsenal
Kocin Arsenal, Mikel Arteta ya yi imanin cewa rashin nasarar da kungiyarsa ta yi a wasanninta da Liverpool da West Ham United a kakar wasa ta bana ta yi tsada a fafatawar neman lashe gasar Premier.
Arteta ya yi magana bayan wasan gasar Premier da Arsenal ta doke Nottingham Forest 1-0 ranar Asabar.