Yanzu haka shirye-shiryen shagalin auren ‘yan masana’antar Kannywood biyu, ya kankama inda za a daura auren jaruma Khadija Yobe wacce aka fi sani da Karimar Izzar So da mawaki Izuddeen M. Doko.
Jarumar ta samu karbuwa ne sakamakon shirin fim ɗin Izzar so mai dogon zamani wanda kowa ya santa.
KU KARANTA: Wata kotun musulunci ta datse igiyar auren ɗiyar Gwamna Ganduje
Kuma ana matuƙar yaba mata kan yadda take shigar mutunci da kuma mu’amala mai kyau tare da abokan sana’arta.
Kamar yadda Mujallar Fim ta bayyana an fitar da hotunan da masoyan suka yi kafin aure wanda mutane da dama suka dinga yi musu fatan alkhairi bayan ganinsu.
Za a daura auren ne a ranar Juma’a, 10 ga watan Fabrairun 2023 a daidai masallacin Juma’a da ke anguwar Nasarawa a garin Damaturu, babban birnin Jihar Yobe.
Ana sa ran daurin auren na rana ne, don kamar yadda katin ya nuna, za a daura ne karfe 2 daidai. Allah ya sanya alkhairi kuma ya ba da ikon halarta, Amin.
Sanata Uba Sani Ya Halarci Daurin Auren Yar Sarkin Zazzau Ambasada Ahmad Bammali
Dan takarar gwamnan jihar Kaduna na jam’iyyar APC Sanata Uba Sani ya bayyana farin cikinsa da halartar taron aurin auren Yar Sarkin Zazzau Ambasada Ahmad Nuhu Bammali.
Wannan na cikin sakonsa na fatan alkhairi ga ma’auratan wanda ya aikewa Jaridar DIMOKURADIYYA a safiyar yau.
Sanata Uba Sani ya ce ya hadu da sarkin zazzau mai martaba Ahmad Nuhu Bammali tare da manyan mutane a wajen daurin auren yarsa Gimbiya Fatima Nuhu Bammali.