Matar Gwamanan Sokoto Mairo Tambuwal ta Bukaci Yan Najeriya Dasu Dukufa Dayin Addu’a
Maryam Mairo Tambuwal matar gwamana Aminu Waziri Tambuwal tayi Kira ga Yan Najeriya dasu dage dayin addu’oi kan matsalar tsaro a Najeriya da kuma taimakawa gwamnati don shawo kan matsalar.
KARANTA:- Wutar Lantarki ta Hallaka Wani Dan Karambani a Edo
Ta bayyana hakane a wani bikin kwana biyu da aka gudanar na addu’oi don zaman Lafiya da karuwar arziqi ga kasa Najeriya.
Kamar yadda ta bayyana matsalar tsaro da kuma canjin yanayi yana matukar takurawa Yan Najeriya da Kuma tattalin arziqin Kasar.
Hajiya Mairo Tambuwal tace matsalar tsaro ta lalata harkoki a Najeriya musamman ma a Arewa inda Yan ta’adda sun kore Mutane daga gidajen su, suna diban Dalibai daga makarantu, suna sanya Yan Kauyuka suna hijira dan dole wanda ba Karamar illa ya haifar ga kasar ba.
Hajiya Mairo tace bawai Malamai kadai ba hadda sauran jama’a yazama dole dasu dukufa wajan yin addu’oi don kawo karshen ta’adancin a Najeriya.
Tace ya zama dole a maida hankali da bada goyan baya da addu’oi ga kasar Najeriya domin Allah ya kawowa Kasar Najeriya dauki.
A lokacin baya Hajiya Maryam ta baiwa Yan kauye taimakon kayan aikin Noma ga Matan dake yin noma musamman wadanda yanayi ya kawo ma nomansu matsala.
Tace tayi wannan tallafin don taimaka wajan shawo kan matsalar da suka shiga.
Najeriya kasa daya ce wanda take da matsaloli na canjin yanayi wanda shima ya shafi manoman kasar.
Tace matsalar tsaro shima ya taimaka wajan kawo tsadar kayan abinci a kasar gaba daya.
Comments 1