Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya yi kira ga jama’ar jihar Katsina da ke fama da hare-haren ‘yan bindiga, da su kara hakuri, a daidai lokacin da ya ce jami’an tsaron kasar nan kokarin kara daukar matakan shawo kan matsalar.
Sanarwar ta fito ne daga bakin hadimin shugaban kasa Malam Garba Shehu ya fitar, ya ce “Buhari ya bayar da izinin kaddamar da wani farmaki na musamman a jihohin Zamfara, Kaduna, Katsina da Sokoto domin dakile ayukan ‘yan ta’adda.” Haka kuma ya sha alwashin kara azama kan kokarin kawo karshen ta’addanci.
Sha’anin kalubalen tsaro na kara ta’azzara a jihar ta Katsina, inda a kullum ake samun rahotannin kisan jama’a ko sace su domin karbar kudin fansa, fyade da kuma sace dukiyoyin al’umma, lamarin da ya janyo zanga-zanga a wasu yankunan jihar.
Shehu ya gargadin cewa yin zaga-zanga zai iya kawo koma baya ga kokarin da sojin ƙasar nan ke yi na yaki da ta’addabci a jihar ta Katsina.
A kan haka shugaba Buhari ya yi kira ga katsinawa da su “ci gaba da goyon bayan rundunar soji wacce ta jima tana aikin dakile ta’addanci a fadan kasar nan”.
Hakan dai na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da gudanar da zanga-zanga a jihar ta Katsina bisa alhinin yawan kashe-kashen da ake yi a yankin.