Wata matar aure ta bayyana wata irin cakwakiya da ta sanya kan a ciki, inda ta tsunduma soyayyar wani namiji daban.
Matar auren ta bayyana cewa ta ci amanar mijinta ta hanyar fara soyayya da wani daban a waje, duk kuwa da irin ƙauna da kulawar da yake nuna mata.
KU KARANTA KUMA: So kenan: Hotunan wata kyakkyawar budurwa da mijinta sun ɗauki hankula
Matar auren ta bayyana hakan ne a wata doguwar wasiƙa da ta rubutowa shafin Northern Hibiscus a Facebook.
A cewar ta tayi sa’ar miji wanda samun irin sa a wannan zamanin sai an tona, domin duk wata kulawa da tarairaya da ake nema a wajen miji tana samu.
Ta bayyana cewa kamar da wasa suka fara hira a yanar gizo da wancan, sai gashi ƙaramar magana ta zama babba inda suka tsunduma cikin kogin ƙauna.
Tun tana ɗaukar abin kamar da wasa a tsakanin su har ya kai ga su dukkan su kowa ya kamu da ƙaunar ɗan’uwan sa. Mutumin yayi mata alƙawarin idan ta kashe aurenta zai aureta, inda ta gaya masa cewa bata son zama da kishiya, bai ɓata lokaci ba ya saki matarsa ta gida.
Da ta ga abin yayi mata yawa alhakin sai ƙara yawa yakeyi sai ta gayawa mijinta halin da ake ciki na irin cin amanar da tayi masa, inda ta gaya masa cewa yanzu fa soyayyar wancan tayi mata katutu a zuciya.
Ta bayyana cewa mijinta ya tambayeta ko sun taɓa lalata da wancan ɗin, inda ta gaya masa cewa ba wani abun da ya taɓa shiga a tsakanin su.
A maimakon ya harzuƙa ya ɗauki wani mataki mai ƙwari a kanta sai kawai ya ƙara ninka irin kulawar da yake bata domin ganin ya kwatota daga wanda suke soyayyar.
Inda matsalar take shine da ita wancan ɗin duk suna jin idan babu ɗaya to ba zasu iya rayuwa ba.
A cewar ta yanzu dai ana kokowa ne tsakanin saurayin ta na waje da kuma mijinta wajen ganin sun mallaketa.
Ta nemi da a sanya ta cikin addu’a saboda duk abun duniya ya isheta, domin ganin ta fito daga cikin wannan cakwakiya da ta saka kanta da kanta a ciki.
Ta kuma bayyana cewa tana da yara uku tare da mijinta.