Wani matashi mai suna James Mafabi, ya bayyana yadda yayi wuff da baturiyar matar sa mai suna Gemma Bevington cikin kwana huɗu kacal bayan haɗuwar su.
James Mafabi wanda aka fi sani da Jam jim ya bayyana cewa sun haɗu da matarsa ne a wani wajen taron aure a Namakwekwe, Mbale, a Gabashin Uganda.
KU KARANTA KUMA: Mijina na matuƙar so na amma na kamu da son wani daban, ku taya ni addu’a -Wata matar aure
“Wata ƙawata ta nemi da in zo Uganda domin halartar shagalin bikin aurenta.” A cewar Gemma
Jaridar Legit.ng ta samo cewa Mafabi ya zo wajen ne a matsayin mai ɗaukar hoto da bidiyo ba tare da sanin cewa zai haɗu da rabin ran sa a wajen ba.
Du duka biyun sun bayyana cewa sun daɗe suna addu’ar samun abokan rayuwa, ba tare da sanin cewa a wannan ranar burin su zai cika ba.
“Na tuna cewa na shiga wani ɗaki na tarar da shi cike da ƴanmata na gyaran gashin su. Ina shiga idanuwa na suka yi arba da ita. A cikin zuciya ta wani abu yace min ‘itace matarka'”.
“Har cikin zuciyata ina da ƙwarin guiwar cewa tabbas watarana sai ta zama matata. Na kasance ina addu’a koda yaushe na auri baturiya sai gashi Allah ya amsa mim addu’a ta.” A cewar Mafabi.
Daga wannan haɗuwar ne suka ɗan yi hira ana cigaba da shagalin bikin, insa daga bisani ya bata lambar wayar sa.
“Bayan haɗuwar mu a wajen bikin, mun ɗauki tsawon yinin ranar muna tare. Daga nan washe gari muka tafi birnin Kampala a mota, sannan kafin ta koma Ingila a rana ta huɗu na gaya mata ina son na aure ta, inda kuma ta amince.” Inji shi.
Watanni uku bayan aukuwar hakan, suka fara shirye-shiryen auren su, wanda aka gudanar a ranar 16 ga watan Disamban 2022.
So Kenan: Hotunan wata kyakkyawar budurwa da mijinta sun ɗauki hankula
A wani labarin na daban kuma, wata kyakkyawar budurwa ta ɗauki hankula a yanar gizo bayan ta sanya hotunanta tare da mijinta.
Wani ɗan gajeran bidiyon wata kyakkyawar budurwa da mijinta wanda yake wada ne ya karaɗe yanar gizo, inda dubunnan mutane suka kalle shi.
kyakkyawar budurwar mai diri ta sanya bidiyon ne a manhajar TikTok domin nuna yadda ita da mijinta suke rayuwar jindaɗi a matsayin su na ma’aurata.