Hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta ƙasa (NDLEA) ta cafke wani tsoho mayaƙin Boko Haram, Alayi Madu, da sarkin Kajola, wani gari wanda yake a iyakar jihohin Ondo da Edo, Baale Akinola Adebayo, ɗauke da miyagun ƙwayoyi.
Hukumar ta kuma cafke wasu mutum 35 masu safarar miyagun ƙwayoyi sannan ta kama miyagun ƙwayoyi waɗanda sun kai ton 2.2 a filin jirgin saman Murtala Muhammad dake Legas da kuma wasu jihohi 12 a sumamen da ta kai satin da ya wuce. Rahoton Daily Trust
KU KARANTA KUMA: Ga irinta nan: Budurwa ta koka bayan saurayinta ya ƙi karɓar cikin da ya ɗirka mata
Kakakin hukumar, Femi Babafemi, ya bayyana a ranar Lahadi a birnin tarayya Abuja cewa an cafke Alayi Madu mai shekara 26 ne a ranar Alhamis 9 ga watan Maris akan titin hanyr Abuja-Kaduna ɗauke da ƙwaya wacce ta kai nauyin kilogiram 10, wacce yace ya siyo daga birnin Ibadan na jihar Oyo inda zai kai ta Maiduguri babban birnin jihar Borno, a cikin buhu.
“A bayanan sa, Madu yace ya fito daga garin Banki a jihar Borno, sannan ya shiga ƙungiyar ƴan ta’addan Boko Haram lokacin yana da shekara 9 a duniya a shekarar 2006.” Yace ya tuba inda ya miƙa wuya hannun sojoji a shekarar 2021.”
Daga nan ya samu horar wa kan sauya fasalin tunanin sa a Maiduguri kafin daga bisani aka wuce da shi jihar Gombe. An sallame shi bayan yayi wata shida.”
“Daga nan sai ya tafi birnin Ibadan, jihar Oyo, inda yayi sana’ar achaɓa, kafin ya shiga muguwar sana’ar safarar miyagun ƙwayoyi inda daga ƙarshe ya shiga hannun hukuma a kan titin hanyar Abuja-Kaduna.” A cewar Babafemi
Batun Goyawa Ɗan Takarar Ganduje Baya a Kano, Shekarau Ya Fayyace Gaskiya
Tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Ibrahim Shekarau, yayi ƙarin haske kan sa labulen da yayi da gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje.
An yi ta kace-nace dai tun bayan da aka ga Ganduje ya raka Shekarau zuwa gidan sa bayan sun je sallar jana’izar babban ɗan kwangila, Alhaji Sani Dahiru Yakasai (SDY), a fadar sarkin Kano, ranar Juma’a