- Hukumar NEMA, ta tabbatar da karbar wasu mutane 109 da suka dawo daga kasar Libya.
- An taimaka wa wadanda abin ya shafa dawowa cikin kasar ta hanyar shiga tsakani na Hukumar Kula da Hijira ta Duniya.
- An bukaci wadanda suka dawo da su yi amfani da damar domin zama jakadun albishir ga sauran matasa da ke shirin fita wata kasar.
Hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasa NEMA, a ranar Talata, ta tabbatar da karbar wasu mutane 109 da suka dawo daga Libya a filin jirgin saman Murtala Muhammad dake Ikeja, jihar Legas,Punch ta rawaito.
Ko’odinetan ofishin kula da yankin Legas, Ibrahim Farinloye, a wata sanarwa da ya fitar, ya ce an taimaka wa wadanda abin ya shafa dawowa cikin kasar ta hanyar shiga tsakani na musamman na Hukumar Kula da Hijira ta Duniya.
KARANTA WANNAN: An Kuma: Majalisar Dokokin Wata Jiha Ta Dakatar Da Wani Shugaban Karamar Hukuma
Ya bayyana cewa wadanda suka dawo daga kasar Libya sun iso ne a cikin jirgin Al Buraq Air Boeing 737-800 mai lamba 5A-DMG wanda ya sauka a tashar Cargo Wing na filin jirgin.
Farinloye ya ce, “NEMA ta karbi rukunin ‘yan Najeriya 109 da suka makale daga birnin Tripoli na kasar Libya. Bayanan wadanda suka dawo sun nuna cewa an dawo da mata manya guda 46, yara mata biyu da jaririya mace daya.
“Baya ga wannan, akwai manya maza 52, yara maza hudu da jarirai maza hudu daga cikin wadanda suka dawo.
“Jirgin ya sauka ne da misalin karfe 5.55 na yamma wanda ya hada da wasu marasa lafiya guda biyu.
Babban Daraktan wanda ya samu wakilcin kodinetan ofishin na Legas, Ibrahim Farinloye, ya bukaci wadanda suka dawo da su yi amfani da damar dawowar su kasar domin zama jakadun albishir ga sauran matasa da ke shirin fita waje.
Hukumomin da suka hada hannu wajen karbar mutanen da suka dawo sun hada da Hukumar Kula da ‘Yan Gudun Hijira ta Kasa, Ma’aikatar Lafiya ta Tarayya, Ma’aikatar Lafiya ta Port, Hukumar Kula da Jiragen Sama ta Tarayyar Najeriya da kuma ‘yan sandan Najeriya.”
Da yake karbar wadanda aka dawo da su bisa radin kansu, Farinloye, wanda ya wakilci Darakta Janar na Hukumar, Alhaji Mustapha Ahmed, ya ce maigidan nasa ya mika fatan alheri ga sabuwar gwamnati domin tunkarar kalubalen da kasar nan ke fuskanta tare da aiwatar da dukkan matakan da suka dace zai juya tattalin arzikin al’umma don samun ci gaba mai kyau.
Ya ce, “Alhaji Ahmed ya kuma bayyana cewa shugaban kasa yana aikewa da alkawarin cewa gwamnatinsa ba za ta bar matasa a baya ba a matsayin wani abu na tafiyar da al’ummar kasa wajen hada karfi da karfe da fasahar zamani wadanda su ne babban ginshikin taimakawa kowace al’umma mai ci gaba a duniya.
“Shugaban kasar zai bullo da wata manufa wacce matasa da mata za su taka rawar gani wajen aiwatar da dukkan manufofin.
“Matasa ne za su zama ginshikin duk wani kuduri a wannan gwamnati saboda irin muhimmancin da shugabancin wannan al’umma ya ba shi wajen ganin an samar da damammakin da ke tattare da mafi yawan al’umma.
A wani labarin kuma, APC Yanzu Za Ta Iya Gyara Laifukan Data Aikata A Baya – Wike
Tsohon gwamnan Ribas, Nyesom Wike, ya bayyana cewa gwamnatin jam’iyyar APC ta sake samun damar gyara kura-kuranta.
Tsohon gwamnan ya caccaki PDP da rashin bin ka’idojin shiyya-shiyya wanda ya ce ya janyo musu hasara a zaben shugaban kasa na ranar 25 ga watan Fabrairu.
Jagoran gwamnonin G5 ya bukaci masu suka da su nuna goyon bayansu ga gwamnati mai ci.