• Gwamnatin Yobe ta samu tallafin bunkasa dajin Jakusko Nasari.
• Za ta yi amfani da kudaden ne wurin sulhunta tsakanin Makiyaya da Manoma.
• Runkan bangarorin biyu sun nuna Jin Dadin dangane da wannan lamari.
Ranar Talata, 13 ga watan Yuli shekarar 2021, Komishiniyar Ma’aikatar Noma da Al-barkatun Kasa Dr. Mairo Ahmed Amshi ta jagoranci manyan Jami’an Ma’aikatar, domin ziyarar neman goyon ba ya Mai Martaba Sarkin Bade da kuma Karamar hukumar Jakusko.
Wurin farko da ta soma ziyarta shi ne fadar Mai Martaba Sarkin Bade, Alhaji Abubakar Umar Suleiman inda ta gabatar masa da makasudin ziyarar.
Cikin bayanan ta, Dr. Mairo Ahmed Amshi ta ce, ta zo da abubuwa uku wadanda suka kunshi:
Gabatar da kudirin Gwamnati na farfado da Jangali, gina cibiyar bunkasa kiwon dabbobi a dajin Jakusko Nasari, da kuma dabbaka lamuran wanzar da zaman lafiya tsakanin manoma da makiyaya.
KARANTA WANNAN LABARIN: PDP zata kwace Kujerun wadanda suka koma APC a Nasarawa PDP zata kwace Kujerun wadanda suka koma APC a Nasarawa
“Gwamnatin Tarayya ta bamu tallafin gina cibiyar bunkasa kiwon dabbobi a dajin Jakusko/Nasari dake karamar hukumar Jakusko, don haka muka zo fada neman goyon baya da tallafin ka a matsayin ka na uban kasa”, inji Dr. Mairo Ahmed Amshi.
Da yake maida martani, Mai Martaba Sarkin Bade, Alhaji Abubakar Umar Suleiman ya ce, wannan abu ne da aka dade ana jiran sa, wanda babu shakka idan ya tabbata zai taimaka wa al’uma.
“Muna maraba da duk wani kudirin da zai kawowa mutanen mu cigaba, zamu bada goyon baya a lokacin da ake bukata”, inji Mai Bade Alhaji Abubakar Umar Suleiman.
Daga fadar Mai Martaba Sarkin Bade, Komishiniyar da tawagar ta, su ka zarce zuwa sakatariyar karamar hukumar Jakusko don gabatar da irin sakon da ta zayyana wa Sarkin Bade.
Bayan sauraron bayanai daga bakin Komishinar da sauran ‘yan tawagar ta, Shugaban Karamar hukumar Jakusko Abdullahi Ahmed Garba ya ce, lallai Gwamnati ta zo da babban al-bishir, inda ya ce, akwai bukatar mutanen yankin su fahimci lamarin, kuma su bada hadin kai.
“Muna rokon Makiyaya da Manoma dake cikin wannan daji, da su fahinci wannan abu, kuma su bai wa Gwamnati hadin kai, domin a samu nasarar gabatar da aikin”, kamar yadda ya bayyana.
Su ma a nasu jawaban, shuwagabannin makiyaya wadanda suka halarci taron tarbar Komishiniyar, sun bayyana farin cikin su da nuna goyon baya, inda su kayi godiya ga Gwmnati kan zaban yankin su, a matsayin wajen soma wannan aikin.
Tawagar Komishiniyar, ta kunshi Sakataren din-din-din na ma’aikatar, Dr. Musa Abba Kolere, Manajan Shirin bunkasa kiwon dabbobi na jiha Dr. Idriss Yusuf Madaki, da wasu Daraktoci.
Comments 1