Rundunar sojin sama ƙasar nan ta sanyawa sabon ɗakin matuƙa jirgin saman sashen ayyuka na .usamman na runduna ta 115 da ke Fatakwal dake jihar Ribas, sunan matuƙiyar jirgin yaƙi mace ta farko a Najeriya, marigayiya Tolulope Arotile.
A yayin ƙaddamar da ginin a ranar Talata, Babban Hafsan Sojin Sama na Najeriya, Air Mashal Sadique Abubakar, ya ce sadaukarwar ta zama wajibi domin jinjinawa yadda Tolulope da sadaukar da rayuwarta tare kuma da ƙarfafa gwiwar waɗanda ke aikin yanzu cewa ba za a manta da su ba ko bayan ba su.
“Ina matuƙar farin ciki yau kasancewar mun taru ne a nan domin ƙaddamar da ɗaya daga cikin ayyukanmu, wato ɗakin matuƙa jiragen saman Rundunar Ayyuka na Musamman ta 115 da ke Fatakwal wanda muka sanya wa sunan Tolulope Arotile, mace ta farko mai tuƙa jirgin saman yaƙi a Najeriya, wacce ta rasu ranar 24 ga watan Yulin, 2020 tana da shekaru 24”, inji babban hafsan.
Ya ƙara da cewa matakin ya zo daidai da ƙoƙarin karrama dukkannin waɗanda suka yi fice wajen sadaukar da kai ga ƙasarsu ta hanyar tabbatar da cewa ba a manta da su ba.
“Muna fatan wannan yunƙurin ba wai kawai zai taimaka wajen tunawa da ita ba ne kawai; muna sa ran zai taka rawa wajen ƙara wa yara mata gwiwar mayar da hankali a harkar karatu da yin aiki tukuru har su cimma burinsu a rayuwa su kuma bauta wa ƙasarsu cikin alfahari da sadaukarwa”, inji shi.
Daga nan sai babban hafsan ya yi kira ga mata da su yi koyi da marigayiya Tolulope wajen shiga rundunar, yana mai cewa ba su da wani shamaki kan nasarorin da za su iya samu a ciki.