Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya buƙaci da a sauya fasalin tsarin tsaron ƙasar nan domin kawo ƙarshen matsalar tsaro baki ɗaya.
Mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Babagana Munguno ne ya sanar da hakan ga manema labarai bayan kammala taron majalisar tsaron kasar a fadar Aso Rock.
A cewar Monguno, Shugaba Buhari ya bukaci manyan hafsoshin tsaron kasar su sake dabarun tsaron kasar ta yadda za a shawo kan matsalolin tsaro a yankin arewa maso yammaci da kuma arewa maso tsakiyar Najeriyar.
https://dimokuradiyya.com.ng/pdp-ta-nemi-buhari-ya-yi-murabus-saboda-matsalar-tsaro/
A makon da ya gabata ne Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum ya zargi sojoji da kawo koma baya wajen dakile mayaƙan Boko Haram.
Wannan ya biyo bayan wani hari da ƙungiyar ta kai wa tawagar gwamnan a kan hanyarsa ta zuwa garin Baga domin ziyarar aiki.
Ranar Ltiinin ne ƙungiyar gwamnonin Najeriya ta bayyana goyon bayanta ga Gwamna Zulum sannan ta ce za ta yi taro kan matsalar tsaron tare da ganawa da Shugaba Buhari da hafsoshin tsaron ƙasar.