‘Yan bindiga sun shiga gidan hakimin ‘Yantumaki Alhaji Abubakar Atiku Maidabino, dake karamar hukumar Danmusa a jihar Katsina suka kashe shi har lahira.
Wani mazaunin yankin ya shaidawa wakilinmu cewa, ‘yan bindigar sun shigan mamacin da misalin karfe 12 na dare inda suka kashe shi nan take tare da raunata mai gadinsa Gambo Chakau.
Wannan ya biyo bayan kisan da aka yiwa shugaban jam’iyyar APC na karamar hukumar Batsari Abdulhamid Sani a gidansa dake Sabon-Garin Dumburawa.
Yace ‘yan bindigar sun taho ne a kan babura kuma kai tsaye gidan hakimin suka wuce, wanda suka kashe shi nan take.
https://dimokuradiyya.com.ng/yan-bindiga-sun-kashe-shugaban-jamiyyar-apc-a-katsina/
Rahotanni sun bayyana cewa ‘yan bindigar sun sulale sun tafi bayan da suka kammala mummunar ta’asarsu ba tare sa sun kai farmaki gidan kowa ba.
Jaridar THISDAY ta rawaito cewa an kai gawar mamacin asibitin koyarwa na Danmusa kuma za a yi jana’izarsa yau din nan kamae yadda addinin musulunci ya tanadar.
Kakakin hukumar ‘yan sanda na jihar Katsina SP Gambo Isah ya tabbatar da faruwar lamarin.
Idan ba a manta ba a baya-bayan nan ne dai ‘yan bindigar suka addabin yankunan kananan hukumomin Dutsin-Ma, Danmusa, Safana, Batsari, Sabuwa, Faskari, Kankara, Dandume da kuma karamar hukumar Kurfi, wanda yayi sanadiyyar rasa rayuwa, dukiya, da gidajen mazauna yankunan, wasu kuma yasa su yin hijari zuwa wasu jihohin dake makwabta da jihar Katsina.