Matar da tafi kowa tsufa a duniya ta riga mu gidan gaskiya.
Tsohuwar matar mai suna Lucile Randon, ta kwanta dama ne tana da shekara ɗari da sha takwas (118) a duniya. Rahoton jaridar The Punch ya tabbatar.
KU KARANTA KUMA: Ba al’adar ƴan Afrika bane duƙawa mace domin neman aurenta -Wani mai barkwanci
Kakakin tsohuwar matar shine ya bayar da sanarwar rasuwar ta a ranar Talata, 17 ga watan Janairun 2023.
Lucile Randon, wacce akafi sani da ƴar’uwa Andre, an haifeta a Kudancin Faransa a ranar 11 ga watan Fabrairun 1904.
Ta rasu ne a gidan da take jinya a Toulun, a cewar kakakin na ta David Tavella.
“Akwai bakin ciki mai girma…. amma burinta na ta haɗu da ɗan’uwanta. A wajenta wannan babban ƴanci ne.” A cewar Tavella
An haifi Randon ne a shekarar da birnin New York ya buɗe tashar farko ta jirgin ƙasa na ƙarƙashin ƙasa.
Gwamnoni Sun Gayyaci Gwamnan CBN don Ganawa Kan Sabbin Takardun Kudin Naira
Gwamnonin jihohi 36 sun gayyaci Gwamnan Babban Bankin Najeriya CBN, Mista Godwin Emiefele, don wani taron tattaunawa a ranar Alhamis kan batutuwan da suka shafi sabbin takardun kudin Naira da babban bankin ya bullo da shi.
Shugaban, yada labarai da hulda da jama’a, sakataren kungiyar gwamnonin Najeriya NFG, Abdulrazak Bello-Barkindo, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Talata a Abuja.
Bello-Barkindo ya ce taron, bisa ga gayyatar da shugaban NGF, Gwamna Aminu Tambuwal na jihar Sakkwato ya yi wa Emiefele, zai fara ne da karfe 9.