Wasu mahara sun hallaka mutane akalla 26 cikinsu har da jami’in dan sanda a wasu kauyuka dake karamar hukumar Bungudu ta jihar Zamfara.
Kakakin Rundunar Yan Sandar Jihar Shehu Mohammad ya bayyana cewa yan bindigar sun kutsa garin ne da muggana makamai inda suka yi ta harbin kan mai uwa da wabi a dare Shekaran jiya asabar.
Shehu ya ce kuma haka bai ishe su ba nan da nan suka nufin kauyen Samawa don sake cin karen su babu babbaka, to amma jami’an yan sanda dake aiki a wannan kauye sun taka musu burki.
Wasu daga cikin yan bindigar sun tsira da raunuka munana bayan wanda suka Hallaka.
Wannan hari yana zuwa ne kwana biyu bayan wasu maharan sun hallaka wasu manoma 12 a kauyukan Magami sa Mayaba Jihar.
Comments 1