Hukumar kula da wutar lantarki (NERC) ta ce mutane da ba su samun wutar lantarki ta aƙalla awa 12 a rana ba sa cikin wadanda za a yi wa ƙarin kuɗi.
Ta ce kamfanonin raba wutar (Discos) ba su isa su ƙara kuɗi ba sai sun tattauna da masu amfani da ita, sun kuma riƙa samar da ita na aƙalla awa 12 duk rana.
Shugaban hukumar, Farfesa James Momoh, ya ce, “Duk ma yadda aka yi, ƙarin ba zai shafi talakan Najeriya ba. A dalilin haka ya sa aka ce DisCos su tattauna da masu amfani da wutar bisa tsarin adadin wutar da ake sha”, inji Momoh
NERC ta kuma sharɗanta wa da Discos tattaunawa da masu amfani da wutar, tabbacin yawan wutar da za su riƙa bayarwa; sanya mita a makarantu; da kuma daina kintacen kuɗin wuta fiye da kima.
Sa’annan ƙarin ba zai shafi masu amfani da wutar da bata wuce 50 kilowatts ba, da kuma waɗanda ba su samun wutar da bata kai awa 12 a rana ba.
https://dimokuradiyya.com.ng/majalisa-ta-dakatar-da-shirin-karin-wutar-lantarki-har-sai-2021/
“Ƙarƙashin wannan tsarin na adadin wutar da aka sha, Discos za su iya ƙara kuɗin wutar ne kawai idan suka ƙara yawan awannin da ingancin watar da suke bayarwa a kullum”, inji Momoh.
Sai dai ba a bayyana ranar da Discos za su ƙara kuɗin wutar ba, amma an amince musu fara tuntuɓar masu amfani da wutar da bin sauran hanyoyin karin.
Kamfanonin raba wutar lantarki uku sun gabatar wa NERC canje-canjen da suka yi na tsarin inganta wutar da zai ba su damar ƙara kuɗin wutar.
Ana hasashen ƙarin da kamfanonin suka so yi a watan Yuli zai kai kashi 47 cikin ɗari, amma majalisar tarayya ta dakatar da su kan lamarin.