Wata budurwa ta bayyana a bidiyo tana rusa kuka tare da ba mutane shawarar kiyayar likitocin Jihar Legas sakamakon ayar da ta gani a kanta, Legit.ng ta ruwaito.
Ta bayyana ne inda ta bayyana yadda likita ya lalata mata fuska inda ya mokadar da hancinta ta koma abar zunde a cikin jama’a.
KU KARANTA: Hotunan kyakkyawar budurwa da mijinta sun ɗauki hankali
Ta shaida cewa saurayinta ne ya matsa mata kan sai ta yi aikin idan ba haka ba sai rabu da ita matsawar ta ki amincewa.
Budurwar ta shawarci mutane kan cewa kada su kuskura su tafka irin nata kuskuren kasancewar maimakon a mikar mata da hanci ya kara kyau, sai aka mokadar da shi ya yi kudu.
A bidiyon wanda ta wallafa a TikTok, ta shaida cewa yanzu haka tana cikin matsananciyar damuwa wanda ta rasa inda za ta sanya kanta.
Nan da nan mutane suka fara tsokaci karkashin bidiyon mata yayin da wasu suka dinga tausaya mata kan wannan tsautsayi da ya fada mata.
Wasu kuma sun yi ta kwasar nishadi tare da dariya kan yadda ta koma tamkar wata halitta sakamakon rashin godiya ga Ubangijinta.
Ta Mori Miji: Wata Budurwa Ta Fashe Da Kuka Bayan Ganin Sha Tara Ta Arziƙin Da Mijinta Yayi Mata
Wani matashin ɗan Najeriya ya nunawa sauran mazaje yadda yakamata ace suna yabawa matan su a ranar murnar zagayowar ranar haihuwar su.
Wani bidiyo wanda wani mai amfani da sunan @nesta_surprise8 a manhajar TikTok ya sanya, ya nuna lokacin da matashiyar matar tasa ta fashe da kuka saboda irin ɗimbin kyaututtukan da mijin nata yayi mata.
Matashin yayi amfani da tsaɓar kuɗi har dubu ɗari biyar aka jera su a gabanta sannan ya kuma siyo mata filawoyi masu kyau na dubu ɗari biyu. Jaridar Legit.ng ta rahoto.
Domin tabbatar da cewa tana da hanyar samun kuɗin shiga, sai ya siyo mata sababbin keke Napeb guda biyu.Ya kuma ƙara mata da sabuwar iPhone 14 da agogon lu’u lu’u cikin kyaututtukan.