Hukumar dake kula da abinci da Magunguna ta Kasa, ta amince da wasu sabbin Magungunan cutar Covid-19 guda biyu.
Magungunan sune Moderna da kuma Sputnik, duk Magungunan an amince da su wajan gaggawa. Kamar yadda Jaridar Channel Tv ta wallafa a shafinta
Shugabar hukumar ta NAFDAC, Farfesa Moji Ajeyede, ya bayyana haka a wajan taron karawa juna sani a Abuja ranar Alhamis.
KARANTA:- BIKIN SALLAH: Jami’an FRSC sun turo ma’aikatan su 35,000 don kula da zirga-zirgan jama’a
Ta cigaba da cewa duk da cewar hukumar lafiya ta duniya bata gama amincewa da Sputnik din ba, sai dai Hukumar NAFDAC tayi bicike ta gano amfaninshi yafi rashin sa.
Sauran labarin na zuwa…….
A wani labarin
Kotu ta yanke musu hukunci shekara uku gidan kaso bayan kulle Yarinyar su a firiza
Wata kotun Majistret dake Sokoto ta yanke ma Emmanuel Bassey tare da matar sa Esther Emmanual hukunci shekara uku gidan kaso, biyo bayan kulle Yarinyar su mai kimanin shekaru 12 a cikin firiza har na tsawon wata takwas
Mai shari’ar Shuaibu Ahmad ya kuma sanya musu tarar dubu ashirin da biyar kan wannan mummunan aikin da sukayi.
Sannan ya kara saka musu tarar dubu dari biyu da saba’in da biyar.
Yace an kama ma’auratan dumu dumu da laifin, ya kuma Kara musu zaman gidan kaso na wata sha biyu da kuma tara naira dari, tun da farko dai an yake musu hukunci shekara uku gidan kaso.
Mai shari’ar yace za su fara zaman gidan kasonne nan take.
Ya Kuma baiwa Goodness Emmanuel da Happiness Emmanuel yaran Emmanuel Bassey beli akan 500,000 ko wannen su.
Jaridar Tvcnews ta ruwaito a watan May, 2021, cewar an sanya wata yarinya mai kimanin shekaru sha biyu a cikin firiza.
A dai lokacin makotansu suka kai rohoto ga jami’an Yan sanda aka kubutar da Yarinyar, sannan aka kama wadanda suka aikata laifin.