Zaɓaɓɓen Gwamnan Osun, Adeleke zai karɓi Magoya APC da suka sauya sheka zuwa PDP
A ranar Juma’a ne zababben gwamnan jihar Osun, Sanata Ademola Adeleke a Abeokuta, babban birnin jihar Ogun zai karbi wadanda suka sauya sheka zuwa jam’iyyar PDP.
Jaridar DAILY POST ta gano cewa Adeleke zai ziyarci Ogun ne tare da wasu jiga-jigan jam’iyyar PDP a yankin Kudu maso Yamma.
KARANTA WANNAN LABARIN: Yan takarar APC Kawai Zan Tallata A Zabe Mai Zuwa— Shugaba Buhari
An tattaro cewa Shugaban Jam’iyyar a Ogun, Sikirulahi Ogundele, da sauran mambobin zartaswa na shirin karbar bakuncin zababben gwamnan Osun.
Sakataren Yada Labarai na Jam’iyyar PDP, Akinloye Bankole, ya tabbatar da hakan ga wakilinmu a ranar Laraba.
A cewar Bankole, ‘yan jam’iyyun siyasa daban-daban sun nuna sha’awarsu ta komawa jam’iyyar PDP a Ogun.
“Sabbin mambobin dubunnan da suka nuna sha’awar shiga jam’iyyar sun fito ne daga jam’iyyar All Progressives Congress (APC), African Democratic Congress (ADC), Allied People’s Movement (APM) da sauran jam’iyyun siyasa dake fadin kananan hukumomi ashirin na jihar Ogun. “, in ji Bankole.
Ya kara da cewa fitattun jagororin kowacce kungiya daga cikin jam’iyyar PDP za su gabatar da jawabi a taron kan hukuncin da suka yanke na zaben PDP a matsayin jam’iyyarsu.
A WANI LABARIN KUMA: Masu Zanga-Zanga Sun Tsayar Da Al-amura Cak A Afrika Ta Kudu