Hukumar kiwon Lafiya ta jihar Bauchi ta bayyana binciken da ta gudanarwa a kan yawan mace–macen mata da ake samu jihar, na da alaka da zubar da ciki ba bisa ka’ida ba da wasu ma’aikatan Lafiya ke yi, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mata wanda kimaninsu ya kai 200.
Kamar yadda Jaridar daily trust ta rawaito, hukumar ta ce Binciken na nuna cewa zubar da cikin ne dalilin mace macen da aka samu a karamar hukumar Azare da wasu kananan hukumomi a jihar.
Shugaban hukumar, Dr Rilwanu Mohammed ne ya bayyana hakan yayin da halarci taron wayar da kan mutane a kan harkokin Lafiya da hukumar tasa ta shirya.
Ya kara da ce ba a kammala binciken ba amma sakamakon da aka samu ya nuna cewa zubar da ciki ba bisa ka’ida ba, shi ne sanadin mutuwar kimamin mata 200, inda ya kara da cewa akwai yiwuwar adadin ya dara haka. https://dimokuradiyya.com.ng/likitoci-na-shirin-tsunduma-yajin-aiki/
Mohammed, ya ce mace-macen sun faru ne saboda juna biyu da mata masu aure da marasa aure suka samu kuma suka ziyarci ma’aikatan lafiya da basu kware ba domin cire cikin.
Ya ce “rashin fahimtar muhimmancin bayar da tazarar haihuwa da rashin sanin abinda ya dace a yi a lokacin da aka samu juna biyu ya zama babbar matsala a jihar nan”.
Dakta Rilwanu ya Bukaci iyaye musamman mata su rika koyar da ‘ya’yansu ilimin da ya shafi jima’i domin rage daukar juna biyu da ba a shirya masa ba inda ya ce hakan zai rage mace-mace da wasu hatsarin da ke tattare da cire ciki.