Gwamnatin tarayya ta bada sanarwar bude tashi da saukar jiragen sama na biranin tarayya Abuja da kuma jihar Legas a ranar takwas ga watan Yuli domin zirga-zirgar jiragen cikin gida, kamar yadda ministan sufurin jiragen sama Hadi Sirika ya bayyana a jiya Labara.
Ministan ya ƙara da cewa, za a buɗe filayen jiragen sama na Kano da na Fatakwal da Owerri da kuma Maiduguri a ranar 11 ga watan Yuli.
Sauran filayen jiragen a ƙasar nan kuma, za a bude su ranar 15 ga watan Yuli.
Wannan sanarwa da Ministan ya fitar ta shafinsa na twitter, ya bayyana cewa nan da ɗan wani lokaci kaɗan jirage zasu fara fita domin zuwa ƙasashen ketare.
Filayen jiragen dai sun kasance a garƙame na tsawon watanni sakamakon ƙoƙarin da gwamnati take wajen ganin an daƙilr yaduwar cutar sarƙe numfashi wadda ta zama gobarar-daji ga duniya baki daya.