Fitaccen jarumin Kannywood, Alhaji Balarabe Jaji ya yi karin bayani dangane da yadda aka ga wasu hotunansa a soshiyal midiya kwance a gadon asibiti.
A hoton an ga inda aka makala bandeji a ido da daya wanda hakan yayi matukar tada hankulan masoyansa.
KU KARANTA: Da dumi-dumi jarumin shirin Kwana Casa’in Kafi Gwamna ya rasu
Mujallar Fim ta samu nasarar tuntubar jarumin inda ya tabbatar mata da cewa hotunan na gaske ne ba na fim ba, kuma lallai Idonsa ya samu matsala.
Kamar yadda ya bayyana, an yi masa aiki a ido daya kuma ya samu sauki kwarai.
A cewarsa:
“Ranar 16 ga watan Nuwamban 2022, aka yi min aiki a asibitin kwararru na Haske da ke Kaduna da misalin karfe 2:00 na rana.
“Ina godiya ga masoya godiya. Allah ya saka da alkhairi. Kuma an yi aiki ya kuma yi kyau. Saboda haka addy ta yi matukar tasiri. Allah ya saka musu da alkhairi.
“Aiki biyu aka yi wa idona daya. Kuma an samu nasarar aikin.”
Ganduje Zai Dauki Nauyin Yan Kannywood Zuwa Kasar Indiya
Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje yace gwamnatin sa zata ci gaba da taimakon masu sana’ar shirya fina-finan Hausa da nufin daga likafar sana’ar zuwa babban mataki.
Gwamnan na wannan jawabi ne yayin da sabbin shugabannin kungiyar masu shirya fina-finai (MOPPAN) ta kai masa ziyara a ofishinsa a yammacin yau juma’a karkashin jagorancin sabon shugabanta Ado Ahmad Gidan Dabino.
Gwamna Ganduje yace gwamnatin sa zata samo guraben horaswa ga mambobin kungiyar a kasashen ketare da nufín inganta sana’ar shirya fim wadda a cewar sa mutane da dama ke kallon ta a kaskance sakamakon rashin samun horo da wadanda suka tsinci kansu a ciki basa yi.