Hukumar bada agajin gaggawa ta ƙasa NEMA, ta bayyana cewa mutane dubu sittin da huɗu da ɗari bakwai da sha biyar a jihar Neja ne za su amfana da tallafin kayan abinci daga gwamnatin tarayya.
Babban Daraktan hukumar NEMA, Muhammadu A Muhammed ne ya bayyana haka yayin da yake miƙa kayan tallafin ga gwamnatin jihar ta Neja.
Muhammadu A Muhammed, wanda Daraktan riƙo ne a sashen bada agaji da tsugunarwa na hukumar, Dakta Bandele Onimode ya wakilta ya ce, hukumar NEMA ta fitar da kayan abincin ne daga rumbun adana abinci na ƙasa da sahalewar shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari don rabawa ga marasa ƙarfi don sauƙaƙa musu raɗaɗin annobar Korona.
https://dimokuradiyya.com.ng/hukumar-nimasa-ta-kai-agaji-jihar-zamfara/
Ya ƙara da cewa nau’o’in kayan abincin iri daban-daban ton dubu biyar ne aka samar don rabawa mutane a jihar.
Shugaban hukumar ya nemi gwamnatin ta jihar Neja da ta wayar da kan jama’arta kan hanyoyin magance ambaliyar.
Mataimakin gwamnan jihar, Alhaji Ahmed Mohammed Ketso wanda shi ya karɓi kayan, ya yabawa gwamnatin tarayya tare da roƙonta da ta tallafawa manoman rani a jihar don yaye musu ku5ncin da suka shiga sanadiyyar ambaliyar ruwan da ta shafe su.